Jagoran Juyin Islama:
Bangaren siyasa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana a lokacin wata ganawa da yayi yau din nan da shugaban Majalisar Koli ta kasar Iraki (ISCI) Sayyid Ammar Hakim da 'yan tawagarsa da suke ziyara a nan Tehran cewa, Amurka ba abin dogaro ba ce inda yayi watsi da ikirarin Amurka na cewa tana fada ne da kungiyoyin ta'addanci na kasar Iraki da suka hada da Da'esh da sauransu.
Lambar Labari: 3481024 Ranar Watsawa : 2016/12/11